Abubuwa 5 da suka zama wajibi lokacin sanyi

0 237

Lokacin sanyi a kasar Hausa sau daya yake zagayowa a duk shekara, amma mutane da yawan gaske da zarar ya zo sukan ce gwamma na zafi. Ko menene dalili? Kawai dai dabi’ar dan Adam ce ba a iya masa.

Sanyi dai lokaci ne da yake zuwa da wasu tsarebe-tsarebe da suka hadar da bushewar fata, salancewar abinci da wuri sauyawar yanani da kura da sauransu. Hakan kan haddasa wasu su koma kamar Akuya wajen yin gaba da ruwa tare da komawa sanya kaya na musamman.

Ga jerin abubuwan da ya kamata a basu kolawa ta musamman lokacin sanyi;

Shafa Mai akai-akai

Da yake fata zata na bushewa da sauri ya kamata a dauki mataki na shafa mai me maiko duk bayan lokaci da zarar an ga fatar ta bushe. Kuma ana shafa man lebe don kare tsagerwarsa musamman ga mata.

Cin abinci mai dumi (zafi)

Akwai bukatuwar sha ko cin abinci mai dumi don wartsakarwa kuma samun mai dumi zai iya kara janyo sha’awar ci da yawa.

Sauyawar Sutura

Ba kawai lokacin ne yake sauyawa ba, hatta suturar da ake amfani da ita a lokaci irin wannan kan sauya. Mutane kan zabi yin amfani da kaya masu nauyi don karawa jikinsu dumi da kuma kare shigar sanyin kai tsaye zuwa cikin jinkinsu.

Yawaita shan ruwa

A irin wannan lokaci mutane da yawa kanyi kuskuren kauracewa shan ruwa da tunanin cewa wai jikinsu baya bukatarsa, amma binciken masana ya tabbatar da cewa ana bukatar jiki ya kasance a jike ta ciki, rashin shan ruwa na iya sanya jiki bushewar da zata yi masa illa.

Amfani da Gilashi da kuma takunkumin fuska

Kurar da ake yi a lokacin sanyi ita ce zata tabbatar maka da cewar yana da kyau a sanya irin wadannan abubuwa don su baiwa ido kariya da kuma hanci ko ba don Korona ba.

Allah ya ba mu wucewa lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: