Abdul’aziz Yari ya raba raguna 500 ga makwabtansa masu karamin karfi
Sanata Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara ya raba raguna 500 ga makwabtansa da mutane masu karamin karfi a garin Talata-Mafara da ke karamar hukumar Talata-Mafara a jihar domin gudanar da bukukuwan Sallah Babba.
Shugaban kwamitin rabon kayayyakin, Sha’aya Sarkin-Fawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da ragonan ga wadanda suka amfana a garin Talata-Mafara.
Sarkin-Fawa, wanda jigo ne a jam’iyyar APC a jihar, ya yaba wa tsohon gwamnan bisa shirye-shiryensa na farfado da tattalin arziki al’ummar jihar daban-daban a matakin kasa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Sallar wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma kasa baki daya.