A yau Alhamis ne ake sa ran za a ci gaba da sauraron ra’ayin jama’a kan batun ƙudurin haraji da shugaban Najeriya ya aike wa majalisun dokokin ƙasar
A yau Alhamis ne ake sa ran za a ci gaba da sauraron ra’ayin jama’a kan batun ƙudurin haraji da shugaban Najeriya ya aike wa majalisun dokokin ƙasar, domin dubawa su, kafin a amince su zama doka.
Kwamitin kuɗi na majalisar wakilan ƙasar ya fara zaman ne a a jiya Laraba.
Sada Soli, ɗan majalisar wakilai ne daga jihar Katsina, kuma ɗan kwamitin kuɗi na majalisar, ya yi wa BBC Hausa ƙarin bayani kan zaman, inda ya ce ana ta samun bayanai, sannan ya bayyana cewa akwai wuraren da wasu suka bayyana buƙatar a gyara, musamman batun haraji a kuɗin haraji.