Gwamnatin tarayya ta sake tsawaita umarnin dakatar da karin kudin wutar lantarki na tsawon mako guda tun bayan daukar makamancin matakin mai wa’adin makonni 2 a ranar 28 ga watan satumbar da ya gabata.
Ta dauki matakin ne da fari, biyo bayan ganawa da kungiyar kwadago ta kasa dake adawa da karin kudin, abin da ya kai ga barazanar tsunduma yajin aiki.
Ta kuma dauki sabon matakin a jiya lahadi, yayin ganawarta da kungiyoyin kwadagon na NLC da TUC, wadda sakatarenta Boss Mustapha ya jagoranta.
Ganawar da ta gudana a fadar Mulki ta Villa, tazo karshe bayan cimma matsaya kan amincewa da shawarwarin kwamatin wucin gadi a ranar 8 ga watan Oktoba, da kuma fidda jadawalin kaddamar da shirin.
A wajen ganawar an kuma amince da rabon mitoci miliyan guda a tashin farko domin cike gibin dake akwai.
- Hisba ta kai samame wasu gidajen sayar da barasa uku a jihar Jigawa
- Aƙalla mutane uku ne suka rasu a wani sabon rikicin manoma da makiyaya a Jihar Nasarawa
- Jam’iyyar PDP ta sanar da ɗage babban taron shugabaninta na ƙasa
- Ƙungiyar Tuntuɓa ta Dattawan Arewa ta dakatar da shugaban majalisar ƙolinta
- Za’a dauki matakin kafa ‘yan sandan jihohi a Najeriya
Ana sa ran soma rabon mitocin cikin makon nan karkashin shirin rabon mitocin na kasa baki daya.
An hakikance shirin, zai samar da jimillar mitoci miliyan 6 kyauta ga yan Najeriya karkashin daukar nauyin babban bankin kasa CBN.