A Jigawa marasa galihu 94,710 ne ke cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na kiwon lafiya

0 316

Sama da mutane dubu 94,710 ne ke cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na samar da mafi karancin shirin kiwon lafiya a jihar Jigawa.

Coordinator hakumar JIMA na jihar Jigawa, Mallam Musa Muazu ne ya bayyana haka a jiya a wajen wani taro na wayar da kan jama’a kan mafi karancin bukatu na kiwon lafiya a shiyyar Jigawa ta tsakiya a zauren Mallam Dau Aliyu dake Birnin Kudu.

Ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da mata, yara ‘yan kasa da shekaru biyar masu nakasa, tsofaffi, masu rauni da marasa lafiya.

Malam Musa Muazu ya ce bangaren wadannan mutane ne kawai za su iya yin rajista da shirin

Shima da yake jawabi, kodinetan kungiyar ELIP Initiative Mallam Isa Mustapha Babura ya ce gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Jigawa sun bullo da wasu tsare-tsare na kiwon lafiya ga marasa galihu. Taron wanda kungiyar Jigawa Mutual accountability Forum JIMA and Options suka shirya domin wayar da kan jama’a domin samun damar shiga shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: