‘Yan ƙasar Nijar, aƙalla 300 ne ake zargin hukumomin Libiya sun kama tare da tsare su a cikin wani mawuyacin hali na rashin kula tsawon wata da watanni.
A cikin wani bidiyo da ake ta yaɗawa ta shafukan sada zumunta an ga ɗaruruwan mutanen cunkushe a cikin wani ɗaki suna kira ga hukumomin ƙasar ta Nijar da su kai masu ɗauki.
Shugaban hukumar ƙoli ta ‘yan Nijar mazauna Libya, Alhaji Sani ya tabbatar da cewa bidiyon na gaskiya ne, mutanen an kama su ne wasu a wajen aikinsu wasu kuma sun shiga ƙasar a kan hanyarsu ta zuwa Sabha aka kama su.
Alhaji Sani wanda ya koka da halin da ‘yan Nijar ɗin ke ciki ya ƙara da cewa ba ma a nan kaɗai ake tsare da ‘yan Nijar ɗin a Libya ba akwai wasu ma a babban birnin ƙasar ta Libya, Tripoli waɗanda ya ce tun ma kafin azumi suke tsare.
Ya ce ba abin da ba su yi na ganin hukumomin Nijar sun kawo musu ɗauki sun shiga lamarin a sake su amma hukuma ba ta yi hakan ba.
Yanzu dai ƙungiyoyin fararen hula da na kare haƙƙin bil’Adama a Nijar ɗin sun shiga kira ga gwamnatin sojin Nijar da ta yi abin da ya dace a kan lamarin.
- BBC Hausa