Aƙalla mutum 6 ne suka mutu a wani harin da jirage marasa matuki na Rasha suka kai a birnin Kharkiv

0 314

Aƙalla mutum shida ne suka mutu a wani harin da jirage marasa matuki na Rasha suka kai a birnin Kharkiv na ƙasar Ukraine, kamar yadda jami’an yankin suka bayyana.

Magajin garin Ihor Terekhov ya ce jiragen na Shahed waɗanda Iran ta ƙera sun kai hari a wasu gine-gine da suka haɗa da rukunin gidaje a safiyar yau Asabar.

Ana ci gaba da kai hare-hare birnin Kharkiv, wanda ya ke kusa da kan iyakar Rasha a cikin ‘yan makonnin nan.

Jami’ai a Ukraine sun ce watakila birnin zai iya kasancewa wanda Rasha za ta ci gaba da kai wa hari a nan gaba.

Ya kara da cewa aƙalla mutane 10 ne suka jikkata sakamakon harin.

Hotunan da ba a tantance ba da ‘yan sandan Ukraine suka wallafa sun nuna masu aikin ceto a wurin, tare da ganin gine-gine da suka lalace da kuma waɗanda ke ci da wuta. Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa, an kuma jikkata mutum 10 a harin inda ta ce an yi ɓarna a rukunin gidajen, gidajen mai, da kuma motoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: