Aƙalla mutum 42 ne suka mutu sakamakon ƙyanda a jihar Adamawa

0 171

Kwamishinan harkokin lafiya da ma’aikata, Felix Tangwame ne ya bayyana wa ‘yan jarida jim kaɗan bayan kammala taron majalisar jihar na ranar Juma’a.
Tangwame ya ƙara da cewa cutar ta shafi mazaɓu takwas a Mubi da bakwai a Gombi, inda ya ƙara da cewa “mace-macen sun kai 42 daga cikin mutum 131 da 177 da cutar ta shafa a ƙananan hukumomin Mubi da Gombi da ke jihar.
An ayyana dukkanin ƙananan hukumomin jihar a wuraren da za a iya samun ɓallewar cutar idan ban da Lamurde.

Leave a Reply

%d bloggers like this: