Aƙalla fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja

0 225

Aƙalla fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Naija mai maƙwabtaka da birnin tarayya Abuja, sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya ruguza wani ɓangaren ginin gidan jiya Laraba.

Mai magana da yawun hukumar gyaran hali ta birnin Tarayya, Adamu Duza, a wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis ya ce “sakamakon ruwa kamar da baƙin ƙwarya da ya kwashe awanni 24 yana zuba ya lalata wasu sassan gidan yarin inda fursunoni 118 suka tsere.”

To sai dai wani jami’in gidan yarin ya ce kawo yanzu an samu damar kama fursunonin 10 daga cikin 118 ɗin da suka tsere, inda kuma suke ci gaba da baza komar neman mutum 108.

Leave a Reply

%d bloggers like this: