Ɓarayi Sun Sace Cinikin Sallah Da Aka Yi A Gidan Zoo Na Kano

0 453

Wani abu mai kama da almara shi ne, labarin sace cinikin da aka yi na masu shiga Gidan Zoo na Kano. Tun da farko dai gidan Rediyon Freedom da ke Kano ne ya ruwaito cewa bayan da aka yi cinikin na kwanakin bukukuwan Sallah, wai sai aka nemi kudin aka rasa.

Jami’an gidan Zoo din sun ce wadansu wadanda ba a san ko su wanene ba ne su ka lababo inda aka ajiye kudin, suka washe komai tatas. Ba su bar ko anini ba.Sai dai kuma wasu majiyoyi a gidan Zoo din sun ce, tuni har an damke wadansu daga cikin ma’aikatan da ake zargin da hadin bakinsu barayin suka shigo.

A nasu ɓangaren rundunar ƴan sandan just Kano a ta bakin kakakinta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa sun damke waɗanda ake zargi da aikata wannan ta’asa

Leave a Reply

%d bloggers like this: