Wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai sun sace tsohon shugaban Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya, NYSC, Manjo Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Dakta Nasiru Mu’azu ya tabbatar wa BBC cewa an sace Manjo Janar Tsiga a garin Tsiga da ke yankin ƙaramar hukumar Kankara, ranar Laraba da daddare.
”An sace shi ne tare da wasu mazauna garin 13 ciki har da mata biyu, a lokacin da maharan suka auka wa garin, ko da yake daga baya mutum huɗu sun kuɓuta”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Duk da cewa ƙaramar hukumar Kankara na fama da matsalar ‘yanbindiga, amma garin Tsiga bai saba fuskantar irin wannan matsala ba.
To amma kwamishinan tsaron ya ce a baya-bayan nan sau uku masu garkuwa da mutane na shiga garin tare da sace mutane.
Kwamishinan tsaron ya kuma yi zargin cewa masu tsegunta wa ‘yanbindiga bayanai ne suka tsegunta musu shigar tsohon Janar ɗin zuwa garin ”saboda a ranar Laraba da rana ne ya shiga garin, kuma da daddare suka je suka ɗauke shi”.
”Daga bayanan da muka samu tsohon janar ɗin bai je garin da rakiyar jami’an tsaro ba, ya je ne da direbansa kawai”, a cewar kwamishinan.
Ya kuma ce gwamnati da jami’an tsaro na ƙoƙari domin tabbatar da ceto mutanen da ‘yanbindigar suka sace.