Ƴan majalissun Tarayya ba zasu samu damar amincewa da kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2022 ba
Yan majalisun tarayya ba zasu samu damar amincewa da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2022 ba,
Shugaban majalissar dattawa na kasa Sanata Ahmed lawan ne ya bayyana hakan a jiya laraba.
Kafin hakan dai a jadawalin kare kasafin kudin da majalisar dattawa ta tsara, za’a gabatar da kasafin kudin ranar Talata da Laraba domin amincewa da shi a yau Alhamis.
Rahotanni sun bayyana cewa a halin da ake ciki shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, baya cikin ƙasa, kuma hakan yasa bai kare kasafin kuɗin hukumarsa ba a gaba kwamitin
Ansamu tsaikon ne saboda kasafin kudin da aka warewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da kuma hukumar kidaya ta kasa yayi kadan
Anasa jawabin shugaban kwamitin dubawa da amincewa da kasafin kudi a zauran majalissar ta kasa Sanata Barau jibrin, ya kara da cewa tsaikon ya biya bayan tattaunawar su, da wakilan INEC da NPC inda suka gano cewa kudaden da aka warewa hukumomin yayi kadan a kasafin kudin na 2022.
Idan zamu iya tianwa dai shugaban kasa Muhammadu buhari ya gabatarwa majalissar kasafin kudin 2022 a ranar 7 ga watan oktoba, kasafin da ya kunshi kimanin naira tiriliyan 16.39.
Yanzu haka majalissar ta tabbatar da cewa sai a ranar 21 ga wannan watan zata amince da kasafin.