Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani basarake mai daraja ta ɗaya a jihar Filato.
Basaraken wanda ƴan bindigar suka ɗauka a fadarsa mai suna Sunday Dajep, ya kasance hakimin al’ummar Mhiship da ke karamar hukumar Pankshin na jihar.
Wani ganau ya ce ƴan bindigar sun isa fadar sarkin ne da ke kusa da hanyar Mangu-Shendam da misalin karfe 11 na daren jiya Laraba, inda suka kutsa cikin fadar tare da yin awon gaba da shi.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ta Filato DSP Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna ci gaba da bibiyar sawun ƴan bindigar domin kama su da kuma kuɓutar da basaraken.