Ƴan bindiga sun sace wasu mutane a harin da suka kai wa tawagar ‘yan kasuwa da ke birnin Gwari a jihar Kaduna

0 439

Yan bindiga da ke addabar wasu sassan jihar Kaduna sun sace wasu mutane a harin da suka kai wa tawagar ‘yan kasuwa da ke birnin Gwari a jihar.

An rawaito cewa lamarin ya faru ne a kyauyen Udawa, gaba da garin Buruku na karamar hukumar Chikun ta Jihar Kano.

Manema Labarai sun rawaito cewa lamarin ya rutsa da ‘yan kasuwa 70 wadanda ke tafiya a jerin gwanon motoci 20 karkashin rakiyar ‘yan sanda, a kan hanyarsu ta zuwa cikin Kaduna da kuma jihar Kano.

Ganau sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar jiya Laraba, kuma babu wanda ya rasa ransa, sannan wadanda suka tsere cikin daji sun kira ‘yan uwansu ta wayar tarho domin shaida musu halin da suke ciki.

Rundunar yan sandan Jihar Kaduna ta sanar da cewa tayi nasarar kubutar da mutane 48 daga cikin yan kasuwar da aka yi Garkuwa da su din.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar ta Kaduna SP Muhammad Jalige, ya fadawa gidan Talabijin na Channels Tv cewa, yan bindigar sun farmaki tawagar yan sandan da suke raka yan kasuwar.

Kazalika, ya ce ba’a samu asarar rayuka ba, daga bangaren yan bindigar zuwa yan sandan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: