Ƴan bindiga sun sace kimanin mutane 61 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna

0 302

Ƴanbindigar sun kai harin ne a garin Buda ranar Litinin da daddare inda suka buɗe wuta, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa manema labarai.

Sai dai babu wata sanarwa daga hukumomin jihar da jami’an ƴansanda da ke tabbatar da harin.

Amma mazauna yankin sun ce ƴanbindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin karfe 11:30 na dare suka dinga harbin kan mai uwa da wabi.

Ya ce akwai ƴan’uwansa mutum shida cikin waɗanda ƴanbindigar suka tafi da su. Ya ce ƴanbindigar sun abka garin ne da niyyar tattara mutane da dama amma taimakon jami’an tsaro da suka kawo ɗauki ne ya taƙaita yawan mutanen da suka sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: