Ƙungiyoyin ma’aikatan man fetur da iskar gas na Najeriya, NUPENG da PENGASSAN, sun bayyana ƙin amincewarsu da shirin sabon shugabancin kamfanin NNPC na ɗaukar sabbin manyan ma’aikata daga wajen kamfanin.
A cikin wata wasiƙa da suka aike ranar 4 ga watan Afrilu ga Shugaban Sashen Kula da Ma’aikata na kamfanin, ƙungiyoyin sun ce wannan mataki ba zai ba wa tsofaffin ma’aikatan da suka sadaukar da rayuwarsu damar ci gaba ba.
Sun jaddada cewa kamfanin NNPC na da dubban ƙwararrun ma’aikata da suka cancanci samun ci gaba, kuma ɗaukar sabbi daga waje zai haifar da rashin daidaito da rikici a cikin gida.
Sun yi gargaɗi cewa ko da an nada sabon shugaban kamfanin, ya kamata a mutunta tsarin samun ci gaba na cikin gida, in ba haka ba, za su ɗauki matakin dakatar da ayyuka gaba ɗaya.