Ƙungiyoyin ƙwadago na NLC, TUC da JNC reshen jihar Rivers sun yi barazanar ɗaukar mataki muddin gwamnatin Najeriya ba ta janye dokar-ta-ɓaci a jihar Rivers ba.
Shugabannin ƙungiyoyin na jihar sun nuna damuwa kan tasirin dokar-ta-ɓacin a kan tattalin arzikin jihar da kuma nuna rashin dacewar ta a hukumance.
Matakin ya sanya an kasa biyan albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar, a cewar su.
Ƴan ƙwadagon sun bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da rashin biyan albashin ma’aikatan keta haƙƙin bil’adama ne da ka iya ta’azzara matsalar tsaro da na tattalin arziki a jihar.
Sanarwar da ƙungiyoyin suka sanya wa hannun ta yi kira ga shugaban Najeriya da majalisar dokoki da kuma ɓangaren shari’a da su ɗauki matakan janye dokar nan take tare da mayar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da kuma ƴanmajalisar jihar.
Idan kuma ba a yi hakan ba nan da wani lokaci, a cewarsu, za su ɗauki matakan da ka iya shafar tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.