Ƙungiyoyin Ƙwadago NLC da ta lauyoyi NBA sun soki gwamnati kan mayar da zanga-zanga laifi a Najeriya
Ƙungiyar Ƙwadago NLC da takwararta ta lauyoyi NBA sun gana, inda suka soki lamirin gwamnatin na mayar da zanga-zanga laifi a Najeriya, sannan suka bayyana cewa cigaban ƙasa mai dorewa na ta’allaƙa ne da bin doka da oda a dukkan matakan gwamnati.
Wannan bayanin yana ƙunshe ne a wata sanarwa da NLC ta fitar a shafinta na X bayan tattaunawar da ƙungiyoyin biyu suka yi a hedkwatar NBA a ranar Alhamis 12 ga Satumba a Abuja.
Ganawar ta buɗe wani sabon babin haɗaka tsakanin ƙungiyoyin biyu na ƙwadago da lauyoyi kamar yadda sanarwar ta nuna, inda suka ƙuduri aniyar yin aiki tare domin tabbatar da doka da oda da adalci da samar da daidaito.
Ganawar na zuwa ne bayan ƙurar da ta tashi bayan kama Shugaban NLC Joe Ajaero ta fara lafawa, inda jami’an DSS suka kama shi domin amsa wasu tambayoyin a kan zargin alaƙa da ɗaukar nauyin ta’addanci, cin amanar ƙasar da zamba ta yanar gizo.
Ƙungiyoyin biyu sun yi Allah wadai da matakin na gwamnati, sannan suka yi kira da babbar murya a kan kare ƴancin ƴan ƙasar, wanda a cewarsu yana da matuƙar muhimmanci domin ƙara wa dimokuraɗiyya garɗi.
A ziyarar, Shugaban NLC ya nanata shirinsu na aiki da Ƙungiyar NBA domin tabbatar da kare ƴancin ƴan Najeriya, musamman ma’aikata.
A nasa jawabin, Afam Osigwe, sabon zaɓaɓɓen Shugaban NBA, ya bayyana cewa a shirye ƙungiyarsu take na aiki da NLC a duk abubuwan da suka shafi shari’a, kamar shawarwari da kuma kare ƴan ƙasa da suke marasa galihu kyauta a kotu.
Ya ce wannan ne ma ya sa ya sake dawo da ɓangaren kare mutum a kotu ajalan domin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya na samun kariya a kotu ba tare da la’akari da ƙarfin aljihunsa ba.