Ƙungiyar malaman jami’a zata shiga sabon yajin aiki biyo bayan ƙarewar wa’adin gargaɗi da ta baiwa gwamnatin tarayya
Ƙungiyar malaman jami’a ASUU ta sake yin barazanar shiga yajin aiki biyo bayan ƙarewar wa’adin gargaɗi da ta bai wa gwamnatin tarayya na makonni uku.
Sai dai mambobin ƙungiyar sun yi kira ga ‘yan Najeriya da ke son ci gaban ƙasar da su shiga tsakani a tattaunawarta da gwamnatin.
Malaman sun yi kiran ne jiya Juma’a yayin taron da suka yi a arewaci da kudancin kasar nan, suna masu cewa take-taken gwamnatin ya sa ba su da wani zaɓi illa su dakatar da aiki.
Bayan kammala taron reshenta na Kudu da aka yi a Ibadan, shugaban ƙungiyar a yankin Farfesa Oyebamiji Oyegoke ya ce an ƙure ƙungiyar ne saboda ƙin cika alƙawurran da gwamnati ta yi.
Kazalika yace take-taken gwamnati wajen zaɓar alƙawurran shekarar 2020 da za ta cika maimakon cika su baki ɗaya, babu gaskiya a ciki.
Zaɓar wani ɓangare game da lamura a madadin cika su lokaci guda ba abin amincewa ba ne a wajensu saboda ba zasu sake ɗaukar walwalar abokan aikinsu da wasa ba.
Karo na ƙarshe da ASUU ta tafi yajin aiki sai da ɗaliban jami’a suka shafe wata tara a gida ba cas ba as.