Ƙungiyar makarantun islamiyya a jihar Kano sun bayyana ƙorafinsu akan yadda gwamnatin jihar Kano ta buɗe gidajen kallon bal a faɗin jihar inda kuma ta bar makarantun islamiyya a garƙame.
Wannan ƙorafi ya fito ne daga bakin wasu daga cikin shugabannin Islamiyya Aisha Ibrahim Ɗorayi da kuma Malam Hassan, a lokacin da su ke tattunawa da filin inda ranka da ake gabatarwa a tashar Freedom Radio da ke Kano.
Malaman makarantun Islamiyya sun ce za su yi zanga-zangar lumana ganin yadda gwamnati ta bude gidan kallo amma bata bude makarantun Islamiyya ba.
- An soki yadda aka kafa Kwamatin Kidaya a Najeriya
- Ba da yawunmu wani tsagin tsohuwar CPC ya goyi bayan Tinubu ba – Malami
- Mutum 9 sun rasa rayukansu a Jihar Katsina
- Tinubu ya kara tsawaita ziyarar da yake yi a nahiyar Turai
- Kungiyar Afenifere ta soki matakin da gwamnatin Tinubu ta dauka kan wakar “Tell Your Papa”
- An bukaci Majalisa ta ware Naira biliyan 2 domin bunkasa magungunan gargajiya a Najeriya
Wannan dai yana zuwa ne kwanaki uku da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin buɗe gidajen kallon ball da ke jihar Kano.
Gwamna Ganduje ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gidajen kallo a jihar Kano.
Hakazalika gwamnan ya yi kira ga masu gidan kallon su tabbatar da cewa an baiwa juna tazara a gidajen kallonsu.
A ƙarshe gwamna Ganduje ya ba su gudunmuwar takunkumin rufe baki guda 40,000 saboda suyi amfani da su wajen kalle-kallensu.