Ƙungiyar ƴan fanshon jihar Jigawa ta ce babu kwabo ɗaya da ɗan ƙungiyar yake bin gwamnatin Jigawa bashi

0 361

Kungiyar Yan Fanshon Jihar Jigawa ta ce babu Kwabo daya da dan kungiyar yake bin gwamnatin Jigawa bashi.

Shugaban Kungiyar na Jihar nan Alhaji Umaru Sani Babura, shine ya bayyana hakan a taron bikin ranar tunawa da yan fansho ta Duniya wanda aka gudanar a Dutse babban birnin Jiha.

Shugaban Kungiyar ya tunasar da gwamna Badaru Alkawarin da ya yi musu a watan Maris na wannan shekara, inda ce musu zai kawo sauye-sauye a fannin fanshon su ta yadda suma zasu rika cin gajiyar mafi kankantar albashi na Naira dubu 30.

Alhaji Umaru Sani Babura, ya bukaci Gwamna Badaru ya kalli bukatun yan kungiyar domin fara aiwatarwa.

Kazalika, ya yabawa Gwamna Badaru Abubakar, bisa yadda yake kyautata rayuwar yan fansho a jihar nan, musamman wajen biyan su hakkokin fansho duk wata akan lokaci da kuma biyan giratuti.

Leave a Reply

%d bloggers like this: