Ƙudirin haramci da saka tarar naira dubu 25 ga duk mutumin da aka kama yana ba-haya ko fitsari ko zubar da shara da tofa yawu da majina a tituna da ƙarƙashin gadoji da gine-ginen gwamnati da ma wuraren taruwar al’umma, da majalisar dokokin jihar Kano ta amince da shi, na ci gaba da tayar da ƙura a jihar.
A ranar Litinin ne dai majalisar dokokin jihar ta amince da ƙudirin, inda kuma za ta miƙawa gwamnan jihar domin sanya masa hannu wanda daga nan ne kuma zai zama doka.
Idan har gwamna ya amince da ƙudirin, duk wanda aka samu da laifi kuma ya gaza biyan tarar ta naira dubu 25 to hakan ka iya kaiwa ga kotu ta tasa ƙeyar mutum zuwa gidan gyaran haki da tarbiyya.
Abdulmajid Isa Umar Mairigar Fata ɗanmajalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano, ya ce wannan wani ɓangare ne na ƙudirin dokar ƙawata birnin Kano amma sai jama’a suka fi mayar da hankali kan abin da ya shafi tofar ta tofar da yawu da majina da kuma ba-haya a bainar jama’a.
Jihar Kano dai na fama da matsalar dalar shara da bahaya a bainar jama’a, wani abu da wasu ke ganin ba zai rasa nasaba da rashin ɗa’a a tsakanin al’umma ba.
To sai dai masu sharhi na ganin cewa ya kamata gwamnati ta samar da wuraren zuba shara da na bahaya kafin aiwatar da wannan doka.