Ƙasashe 58 daga cikin 164 mambobin Kungiyar Cinikayya ta Duniya (WTO) sun nuna goyon bayansu ga buƙatar neman shugabar ƙungiyar Ngozi Okonjo-Iweala ta yi tazarce wa’adi na biyu.
Ƙasashen sun bayyana goyon bayansu ne ga Okonjo-Iweala a babban taron ƙungiyar da aka gudanar jiya Litinin, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta na intanet.
Ƙasashen sun jinjina wa shugabar kan nasarorinta da kuma jajircewarta a wa’adinta na farko.
Okonjo-Iweala ta ce ta saurari buƙatar ƙasashen kuma za ta yi nazari game da buƙatar.
Okonjo-Iweala ƴar Najeriya, ita ce ta bakwai a matsayin shugabar Kungiyar Cinikayya.
Ta karɓi rantsuwar kama aiki ne a ranar 1 ga Maris a wa’adin farko na shekaru huɗu kuma wa’adin zai ƙare ne a ranar 31 ga Agustan 2025.
Tsohuwar ministar kuɗin ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka da ta taɓa rike muƙamin shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya.