Ƙasar Ghana za ta ci gaba da rufe iyakokinta har sai abin da hali ya yi sakamakon guje wa ɓullar korona karo na huɗu
Ƙasar Ghana za ta ci gaba da rufe iyakokinta har sai abin da hali ya yi sakamakon guje wa ɓullar korona karo na huɗu.
Shugaban ƙasar ta Ghana Nana Akufo- Addo, shine ya bayyana hakan yayin wani jawabi inda ya ce gwamnatinsa tana sa ido kan irin barazanar da cutar ke yi da kuma yadda ake riga-kafin cutar a wasu ƙasashe kafin ta buɗe iyakokinta.
Tuni de mazauna wasu garuruwa da ke makwaftaka da kan iyakokin suka soma zanga-zanga sakamakon lokaci mai tsawo da aka ɗauka iyakokin a garƙame.
Manyan motocin kaya da ke kan hanya ne kaɗai aka amince ma wa su wuce.