Karamar Hukumar Guri ta samar da cibiyoyin rigakafin cutukan dabbobi guda shida a yankin
Cibiyoyin sun hadar da Bodala Fulanin Adiyani da Matarar Kano da Safani da Kadira da Lafiyari da Zugobiya
Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Musa Shuaibu Muhammad yace Karamar Hukumar a shirye take wajen kula da lafiyar alumma da dabbobi domin kara samun koshin lafiya da madara da Nono da kuma Nama
Ya umarci alummar yankin dasu bada hadin kai da bada goyan baya ga maaikatan rigakafin cutar corona domin samun nasarar da ake bukata
Alhaji Musa Shuaibu Guri yace karamar hukumar ce ta ke matsayi na biyar a aikin rigakafin cutar corona.