Ƴan NYSC na Jigawa sun zama abin misali, sun guji zanga-zanga – Ko’odineta

0 272

Ko’odinetan Jihar Jigawa na Shirin Hidimtawa Kasa (NYSC), Alhaji Dawud Jidda, ya yaba wa ‘yan hidimar kasa a karamar hukumar Hadejia kan kyakkyawan halayensu da kuma yanke shawarar gujewa zanga-zangar da ta faru kwanan nan. Ya yi wannan bayani yayin ziyararsa zuwa sakatariyar NYSC ta karamar hukumar a yau da safe.

Ko’odinetan jihar da tawagarsa sun samu tarba daga jami’an shiyya, jami’in karamar hukuma, da ‘yan hidimar kasa a sakatariyar.

Dawud ya bayyana cewa wannan ziyara ce ta duba yadda ‘yan hidimar kasa ke aiki. Ya kuma jaddada bukatar tabbatar da cewa ‘yan hidimar kasa ba su shiga rikicin zanga-zangar ba kuma ba su aikata wani nau’in karya doka ba, musamman a Hadejia, wanda ke daya daga cikin wuraren da suka fuskanci ɓarna a jihar.

Ko’odinetan ya yaba wa ‘yan hidimar kasa na Hadejia kan jajircewarsu, sadaukarwa da kuma ladabi wajen sauke nauyin da ke kansu. Ya kara da cewa bai samu wani koke ko rahoton rashin kyautatawa daga gare su ba, wanda ya bayyana hakan a matsayin abin kwarai.

A karshe, ya yi kira ga ‘yan hidimar kasa su kasance masu kishin kasa, ladabi, da gaskiya, su kuma zama jakadu nagari na NYSC ba kawai a lokacin shekarar hidimarsu ba har ma bayan sun kammala.

Leave a Reply

%d bloggers like this: