Ƙungiyar Kwadago ta nemi Gwamnati ta hukunta jami’an tsaron da suka mamaye ofishinsu

0 187

Ƙungiyar Kwadago ta (TUC) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki mataki kan waɗanda suka bayar da umarni da kuma waɗanda suka aiwatar da mamayar da aka kai wa Shalƙwatar Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) da ke Abuja kwanan nan. 

Shugaban TUC, Mista Festus Osifo, ya bayyana damuwarsa game da lamarin, yana mai cewa abin ya saɓawa haƙƙoƙin ɗan Adam, musamman ‘yancin yin magana da bayyana ra’ayi.

Osifo ya yi kira da a gudanar da binciken gaggawa da samar da cikakken bayani kan lamarin, yana mai jaddada cewa wannan mamayar tana nuni da wuce gona da iri da jami’an tsaro suka yi, kuma tana barazana ga haƙƙoƙin ‘yan Nijeriya. Ya kuma buƙaci a maido da duk wasu kayan da aka kwace da gaggawa, tare da neman a ba da cikakken bayani kan abin da ya kira da (ɗaukar) mataki mara tushe.

NLC ta tabbatar da wannan mamayar, inda ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kutsa kai cikin ofishin ta na ƙasa, suka kama masu gadin ofishin, sannan suka tilasta shiga wasu ofisoshi a bene na biyu.

Kakakin NLC, Benson Upah, ya ce jami’an tsaron sun yi barna a wurin sayar da littattafai sannan suka yi awon gaba da ɗaruruwan littattafai da sauran kayan bugawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: