Ƙudirin da ke neman ƙirƙiro sabuwar jiha a kasar nan ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai

0 178

Ƙudirin da ke neman ƙirƙiro sabuwar jiha a yankin kudu maso gabas ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai.

Ƙudirin yana neman a ƙara jihar Etiti a yankin mai jihohi biyar kuma ‘yanmajalisa Amobi Ogah (LP, Abia), Miriam Onuoha (APC, Imo), Kama Nkemkama (LP, Ebonyi), Chinwe Nnabuife (YPP, Anambra), da kuma Anayo Onwuegbu (LP, Enugu) ne suka gabatar da shi.

Ogah ya ce niyyarsu ita ce kawo ƙarshen abin da aka daɗe ana tattauna a kai na yawan jihohi a yankin nasu. Suna so ne a yanki jihar daga jihohin yankin na Anambra, Imo, Ebonyi, Abia, and Enugu.

Yayin zaman na jiya Alhamis, an amince da ƙudirin ne a mataki na biyu ba tare da wata muhawara ba daga ‘yanmajalisar, inda suka amsa amincewa lokacin da Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas ya nemi kaɗa ƙuri’a da baki.

A ranar Laraba ma Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar da ƙudirin neman ƙirƙiro jihar Tiga daga Kano a arewa maso yammacin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: